Shugabar kungiyar, Joanne Lui ta yi kira da kasashen duniya su kara hada karfi waje guda karkashin jagorancin Hukumar lafiya ta Duniya, domin tunkarar cutar.
Ta kara da cewa shawo kan cutar ta Ebola a kasar Liberiya inda aka samu mutuwar fiye da mutane 300 na da matukar muhimmanci wajen magance barkewar annobar ta Ebola.
"Dole ne gwamnatoci su dauki matakai a halin yanzu, idan har muna son mu kawo karshen annobar" A cewar Ms Lui ABNA